UWA ABAR KOYI: Barrister Hauwa Bello Hayyatu

0
613

Daga Jazuli Lawan Gwarzo

INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJIUN, Lallai mutuwa tana yanke jin dadi ta raba kowa da masoyi! Allah ka gafartawa Mama Kuye.

Hakika nayi rashin Uwa, Aminiya, Malama, Mashawarciya, Mai ilimi hakuri da hangen nesa wadda ta kasance katanga mai karfi da ta kare min abubuwa da yawa.

A rayuwata na dade banga mace jajirtatta kamar Mama ba, tun daga lokacin da take makaranta a Legal har Jami’ar Bayero har zuwa Nigerian Law school a Legas daga dakin mijinta tayi dukkan karatunta, tare da haifar “Yayanta gaba daya cikin wannan hidima, har ila yau, ta gama karatun ta ta koma dakin mijinta ba tare da yin aiki ko tunanin aiki ba, illa sana’o’i wadanda mata ke iya yi daga dakunansu domin rufawa Kai asiri. Wannan Baiwar Allah cikin yardar Allah ta karfafe ni cikin neman ilimi komai wahalarsa, tareda koyar dani kasuwanci daban daban domin Dogaro dakai. A karshe karshen Shekaru 90s zuwa 2000s gurin Ki na fara samun cassette na complete Qur’an na Sheik Sudais da Sheik Shuraim Da Sheik Huzayfi, Kuma ban san wanda ya fiki yawan kasa kasai na Sheik Jaafar da Umar Sani Fagge, har wadanda a yau baa samunsu. Kece kika koya min yin Saukar Alqurani mai girma cikin watan Ramadan, Innalillahi wa inna ilaihir rajiun! Allah ya kar6a miki.

Ana kara gane halin mutane idan tafiya ta hada ka dasu ( komi alakarka dasu) cikin ikon Allah nayi tafiye-tafiye da ita daban-daban har kasashen waje musamman ayyukan Haji da Umara. A tafiya ta koya min Karamci. Har bana iya banbance karamcinta tsakanin na gida dana tafiya. Shekara Biyu dasuka wuce munyi tafiya ni da abokina, muka sameki a Dubai har Airport kika tura Yahaya Tanko ya dakkomu Don kar musha wahala, sannan kika yimana Cikakkiyar kar6ar baki.

Abin mamaki cikin wannan jinyar akayimin haihuwa Amma Karima sai da ta aiko min Da ragon Suna karo na hudu! Ba rabo da gwani ba…….

Bana mantawa a shekarar 1999 Munyi shiri tsaf domin komawa Abuja, Amma kash saboda hangen nesanki kikace sam, sakamakon rashin makarantu masu inganci a wancan lokacin musamman makarantun Islamiya wanda yanzu na fahimci fikihunki Mama, Domin kuwa Zainab, Hayatu, Ummukulsum, da Amina a yau daga Engr sai Likita sai Pharmacist, gakuma mu duk kowa ya tsaya da kafarsa, har cikin maaikatan gidan Mama yau an sami wadanda sukaje da Kuma wadanda ke hanyar Jami’a,Alhamdulillah.

Baiwar Allah mai fadin gaskiya komai dacinta, Sati Biyu munyi doguwar tattaunawa wadda takunshi abubuwa da yawa da baki ta6a gayamin irinsuba, ashe bankwana mukeyi, wadanda ba na rubutawa a wannan kafar bane, Amma InshaAllah naji na kuma dauki dukkan abubuwan kika gaya min UWATA!

Ya Allah ka azurtamu da hakuri irin nata, Ya Allah Ka kar6i ayyukanta na Alkairi, ka shafe Sayyi’arta, Ya Allah Ka sada ta da Salihan Bayinka, da Shahidai, Ya Alla ka sanya ta a Aljannatul-Firdausy aala.

Allaahum-maghfir laha warhamha, wa ‘aafiha, wa’fu ‘anha, wa ‘akrim nuzulaha, wa wassi’ mudkhalaha, waghsilha bilmaa’i waththalji walbaradi, wa naqqiha minal-khataayaa kamaa naqqaytath-thawbal-‘abyadha minad-danasi, wa ‘abdilha daaran khayran min daariha, wa ‘ahlan khayran min ‘ahliha, wa zawjan khayran min zawjiha, wa ‘adkhilhal-jannata, wa. ‘a’ithhu min ‘athaabil-qabri wa ‘athaabin-naar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here