Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Faɗaɗa Dokar Hana Zirga-Zirga Ta Sa’o’i 24 A Faɗin Jihar Gabaɗaya

0
186

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya faɗaɗa dokar hana zirga-zirga ga ilahirin faɗin jihar, biyo bayan aika-aikar wasu ɓata gari da sunan zanga-zangar EndSARS.

A wata sanarwa da kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro, Samuel Aruwan ya fitar, ta ce gwamnatin jihar ta ɗauki matakin ne don kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

“Gwamnatin jihar Kaduna ta faɗaɗa dokar hana zirga-zirga ta awa 24 a faɗin jihar wacce da farko a ka sanya a ƙananan hukumomin Chikun da na Kaduna ta kudu.

“An ɗau wannan matakin ne don taimakawa wajen kare al’ummar mi, kare rayuka da dukiya.

” Faɗaɗa dokar hana zirga-zirga ta awa 24 ga dukkan kananan hukumomi 23 na jiharnan ta fara aiki ne nan take.

“Gwamnatin jiha na yin kira ga mazauna jiharnan da su bawa gwammati hadin kai a yayin da ake daukar matakan da suka dace don tabbatar da doka da oda da kuma kare hakkin yan kasa na rayuwa cikin salama”, Inji Aruwa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here