An Kafa Dokar Hana Fita ta Tsawon sa’o’i 24 a Kuros Riba

0
105

Daga Musa Kutama, Kalaba

Bayan shafe wunin juma’a da ta gabata da matasa masu zanga-zangar #Endsars suka Yi tare da fasa Dukkanin shaguna da gwamnatin kuros riba ta adana kayan abinci na rage radadin cutar kurona da gwamnatin tarayya ta bayar masu zanga-zangar sun kona dukanin wuraren bayan da suka kwashi-na kwasa suka bankawa wurin wuta.

 

Babban shagon adana kayan abinci dake harabar hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kuros Riba wato SEMA sun kwashi nau’in kayan abinci irin su Masara,Garin kwaki,shinkafa,sauran sune Taliyar indimie ,Wake da Garewanin manja da mangyada .

 

Lamarin da ya jefa mazauna Kalaba Babban birnin jihar cikin firgici.

An shafe Daren Asabar anajin harbe-harben bindigogi tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zangar.

Wannan ne ya Sanya gwamnan Jihar Kuros Riba Farfesa Ben Ayade ya kafa dokar hana fita ta tsawon Awa ashirin da hudu a fadin Jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here