Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Kano wato FCE, ta sanya ranar Litinin 2 ga watan Nuwamba a matsayin ranar komawa karatu.
Kwalejin ta ce komawar ta shafi masu karatun NCE da yan Part-Time da kuma masu Pre-NCe.
Hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da mataimakin magatakardar kwalejin kuma shugaban sashin hulda da jama’a na kwalejin, Auwalu Mudi Yakasai ya fitar a yau Juma’a.
Sanarwar ta ce, hukumar kwalejin na umartar dukkan daliban da za su koma da su bi ka’idojin kariya daga cutar COVID-19.
“Ana saran dukkan dalibai za su sanya safar rufe hanci da baki yayin da za su shiga makaranta”, inji sanarwar.