An Kafa Kwamitin Binciken Ayyukan Rundunar SARS a Jihar Katsina

0
89

An kaddamar da kwamitin da zai binciki ayyukan da rundunar SARS da aka rushe suka yi a jihar Katsina.

Kwamitin na mutane 11 na karkashin jagorancin, Mai shari’a Abbas Abdullahi Bawale na babbar kotun jihar Katsina.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da, AIG Danlami Yar’adua mai ritaya, Alhaji Mustapha Ibrahim Zango, Alhaji Bello Musa Dankano, Farfesa Usman Dhun-nurain, Hajita Rabi Mohammed da Ibrahim Ahamd Katsina.

Ragowar sun hada da Barista Dikko Abbas, Aliyu Usman sai Alhaji Ibrahin Muhammad Daku wanda shi ne Sakataren kwamitin.

Yayin jawabi lokacin kaddamar da kwamitin, Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya bukaci kwamitin binciken ya gano jami’an rundunar SARS wadanda suke da hannu a cin zarafin wani.

Sannan ya bayyana ayyukan da kwamitin zai yi da suka hada da bayar da shawarwari kan hukuncin da yakamata a dauka kan wadanda aka samu da laifi tare kuma da samar da matakan hana faruwar hakan nan gaba.

Ya kuma sanar da cewa kwamitin yana da makwanni 8 don mika rahotan sa.

Gwamna Masari ya ce bayan rusa rundunar SARS shugaba Buhari ya bada umarni ga gwamnonin jihohi da su kafa kwamitin bincike kan ayyukan rundunar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here