#Zanga-Zangar EndSARS: Buhari Ya Aika Saƙo Ga Kasashen Ƙetare

0
267

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga kasashen ketare da su dinga cikakken bincike kafin su yi magana kan batun da ya shafi kasarnan.

A jawabin da ya gabatar ga yan Najeriya a daren yau, Buhari ya ce Gwamnatin sa ba za ta bari a ci gaba da karya doka da oda ba.

Ya kuma bayyana nadamar sa bisa rasuwar rayuka tare da kira ga masu zanga-zangar EndSARS su bar kan tituna.

“Ya zama dole gare ni na yi muku jawabi bayan na kammala tattaunawa da manyan hafsoshin tsaro”, inji shi.

“Ga makotan mu da kungiyoyin kasashen duniya, dayawan su da suka bayyana damuwa kan abinda ke faruwa a Najeriya, mun gode muku kuma muna kira a gare ku, ku dinga neman samun bayanai cikakke kafin ku dau wani mataki tare da fitar sanarwar cikin gaggawa”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here