Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Na Jagorantar Zaman Majalisar Tsaron Kasa

0
151

Yanzu haka shugaban kasa Muhammadu Buhari na jagorantar zaman majalisar tsaron kasa a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Zaman ya samu halartar mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, Sakataren gwammatin tarayya, Boss Mustapha, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da mai ba wa shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro, Babana Monguno.

Haka kuma shugabannin hukumomin tsaron da suka halarta sun hada da babban hafson tsaron kasa, Janar Gabriel Olanisaken, Babban hafson sojin kasa, Janar Tukur Buratai, Babban hafson sojin ruwa, Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas da babban hafson sojin sama, Air Mashal Sadique Abubakar.

Haka kuma babban sufeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu, da Daraktan hukumar tsaro ta farin kaya, Yusif Bichi , Daraktan hukumar bayanan sirri na kasa, Ahmed Rufa’i sun halarci taron.

Ministocin da suka halarci taron sun hada da, Ministan Tsaro, Bashir Magashi, na cikin gida, Rauf Aregbesola, na hukumar yan sanda, Mohammad Dingyadi da ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama.

Taron na zuwa ne bayan rikicin da aka samu sakamkon zanga-zangar EndSARS.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here