Ƴan Daba Sun Sake Ƙone Ofishin Ƴan Sanda a Jihar Legas

0
184

Yan daba sun sanyawa ofishin yan sanda na Ojodu dake yankin Beger a jihar Legas wuta yau Alhamis.

Rahotanni sun bayyana cewa an kone ababen hawa guda bakwai.

Wani shaidar gani da ido mai suna Idowu Jamiu, ya shaidawa wakilin jaridar The Punch cewa yan daban sun kuma sace kayayyakin shagunan dake kusa da ofishin.

Wani mai shago a wajen, Mai suna Iya Agbo, ya ce “Sun fasa shagunan dake kusa da ofishin yan sandan. Sun sace tare da lalata kayan mu na miliyoyin kudi”.

Rahotanni sun bayyana cewa tun ranar Laraba yan daban su ka yi yunkurin kona ofishin amma ba su samu nasara ba.

Jami’an kashe gobara suna wajen da abun ya faru don kashe wutar da ke ci.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here