Sabon Shugaban Jami’ar Yusuf Maitama Sule Kano Ya Kama Aiki

0
187

Daruruwan Dalibai, Malamai, da ma’aikata ne su ka raka sabon shugaban jami’ar Yusuf Maitama Sule Kano, Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa zuwa ofis a yau Laraba.

A ranar 17 ga watan Oktoba ne dai majalisar gudanarwar jami’ar ta Yusuf Maitaima Sule Kano ta nada Farfesa Atiku Mukhtar Kurawa a matsayin sabon shugaba n jami’ar.

Yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan karbar ragamar kama aiki, Kurawa ya ce, a shirye yake ya yi maganin matsalolin da suke addabar jami’ar kamar yadda ya warware matsalolin kwalejin fasaha ta Kano.

Ya kuma bayyana cewa zai hada kai da Malamai da ma’aikatan jami’ar wajen ciyar da ita gaba.

Sannan ya yabawa gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje bisa goyan bayan da yake bawa fannin ilimi.

Kafin nadin nasa dai, Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa, shi ne shugaban kwalejin fasaha ta jihar Kano.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here