Fusatattun Matasa Sun Yi wa Gidan Bola Tinubu Ƙawanya

0
219

Fusatattun matasa sun yi wa gidan tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu ƙawanya, tare da yunkurin kutsawa gidan.

Gidan ya na Bourdillon dake Ikoyi a jihar Legas.

Tun bayan da aka yi zargin cewa jami’an tsaro sun bude wuta kan masu zanga-zanga a jiya Talata a Birnin Legas abubuwa suka kara rincaɓewa.

Wasu dai na zargin Bola Tinubu na da hannu a kisan da ake zargin sojoji sun yi kan masu zanga-zangar, sai dai Bola Tinubu ya musanta zargin tun da fari.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here