Ƴan Bindiga Sun Hallaka Mutane 22 A Jihar Zamfara

Daruruwan ƴan bindiga a kan babura sun afka garin Tungar Kwana dake karamar hukumar Talatar Marafa a jihar Zamfara da misalin karfe 11 na dare a jiya Talata inda suka kashe mazauna kauyen 22.

Wani wanda ya tsira daga harin, mai suna Maigora, ya shaidawa jaridar New Telegraph cewa, yan bindigar da yawun su ya kai 150 a kan babura, sun afka garin tare da fara harbi kan mai uwa da wabi lamarin da ya kai ga asarar rayuka 22 maza da mata.

“Yawancin mutane sun tafi makwanci yayin da maharan suka kawo harin, an kashe yara kanana da mata yayin da suke kokarin guduwa, abin da kawai ake ji shi ne wata murya dake umarnin kashe duk wani abu mai motsi har kaji da tsintsaye.

“Duk da rufe hanyoyin guduwa da yan bindigar suka yi, Dayawan mazauna kauyen sun sun gudu zuwa dazuka, sun buya anan har zuwa safiya” inji Maigora.

Shima wani da ya tsira, mai suna Malam Mustapha, ya ce jama’a da dama sun samu raunika sakamakon harin.

Ya kuma yi bayanin cewa, yan bindigar sun sace shanu da tumaki a kauyukan.

Malam ya kuma yi kukan cewa, daruruwan mutanen da suka gudu zuwa daji suna dauke da raunuka sun firgta yayin da suka fantsama basu san inda suka nufa ba wanda hakan ka sanya su fada sansanonin yan bindigar.

“Da yuwuwar yan bindigar su dawo kauyen, kowa ya bar gidan sa, saboda yan bidigar sun yi barazanar dawoaa” inji shi.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda reshen jihar Zamfara, Mohammed Shehu, ya tabbatar da kisan mutane 20 a kauyen ba 22 ba”.

Shehu ya yi bayanin cewa yan bindigar suna jin haushin mazauna kauyen ne bisa goyan bayan da suke bawa jami’an tsaro wanda ya kai ga hallaka yan bindigar da dama a makon da ya gabata.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here