Yadda Aka Lalata Ababen Hawa Tare Da Sace Kayan Shaguna A Yankin Sabon Gari Dake Kano

0
151

Zanga-Zangar EndSARS da ke ci gaba da gudana a manyan biranen Kasarnan ta koma rikici a Kano yayin da aka ƙone ababan hawa 15 da lalata shaguna da dama.

Rahotannin sun bayyana cewa da misalin karfe 1 na rana zanga-zangar ta koma rikici a titin Sarkin Yaki zuwa Court Road zuwa Zangeru a yankin Sabon Gari kafin ƴan sanda su shawo kan lamarin.

Rahotannin da ba a tabbatar ba sun bayyana cewa, mutane biyu sun rasu yayin zanga-zangar.

Wani wanda abun ya faru a kan idon sa kuma ya nemi a boye sunan sa ya ce an ƙone ababan hawa 15 tare da sanya wuta a wajen bauta.

“Zaka iya kalla da kan ka yadda hayaki ke tashi daga Titin Igbo Road sannan zaka ga yadda matasa su ke riƙe da sanda don kare kan su daga harin yan daba”.

Motoci biyu dake bakin shagon Galaxy Mall na Sabon Gari an ƙone su sannnan ɓata garin sun sace kayayyakin dake shagon.

Haka kuma, a titin Airport Road, an ga motoci a kone a gaban Makarantar Sakandire ta St. Thomas da kuma wata a titin Hausa Road.

An bayyana cewa sa’o’i kadan bayan ƴan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga, yan daba sun kutsa kai tare da fara sace dukiyoyi, kona motoci tare da kona tayoyi.

 


Rikicin ya kaure ne yayin da wasu masu zanga-zangar sun iso Sabon Gari tare da sanya wuta a kan ababen hawa.

Rikicin ya yaɗu zuwa wasu yankunan da wajen cin abinci na Chicken Republic da ke yankin wanda aka lalata shi.

Kwamishinan yan sanda na jihar Kano, Habu Sani ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce an kone ababan hawa 7 tare da lalata 8 da kuma kone babura biyu.

Kwamishinan yan sandan ya kuma tabbatar da cewa an lalata wajen shakatawa a Hausa Road.

Ya kuma bayyana cewa mutane biyar sun samu raunuka.

Habu Sani ya ce an kama mutum daya wanda kuma likita ne tare da samun makamai a wajen sa yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.

Ya ce ” Masu zanga-zangar sun yi shirin zuwa gidan gwamnati amma sai suka sauya inda za su je zuwa titin Airport wanda hakan ya haifar da rikicin.

“Mun samu nasarar kare rayuka, wajen bauta da makarantu. Mun tura jami’an mu yankin don tabbatar da kare dukiya da lafiyar al’ummar”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here