Wasu Da Ake Zargin Ƴan Daba ne Sun Ƙone Ofishin Ƴan Sanda a Jihar Oyo

0
194

Wasu da ake zargin yan daba ne a yau Talata sun kona ofishin yan sanda na Ojoo dake jihar Oyo.

An kone motoci da dama a ofishin yan sandan.

Rahotannin sun bayyana cewa rikicin ya fara ne bayan zargin cewa jami’an yan sanda sun bude wuta yayin zanga-zangar EndSARS.

Bayan hakanne, wasu yan daba suka kaddamar da hari a ofishin yan sandan tare da kunna masa wuta.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here