Wani Jigo a APC Ya Nemi Kotu Ta Hana Amfani Da Shafin Twitter a Najeriya

0
81

Babban Jigo a jami’iyyar APC, Adamu Garba ya bukaci Babbar kotun tarayya dake zaman ta a Abuja,  ta dakatar da kamfanin Twitter daga yin aiki a Najeriya.

Adamu Garba tun da farko ya soki shugaban kamfanin Twitter kuma wanda ya kafa ta, Jack Dorsey bisa zargin samar da wata mahada ta tara tallafi ga masu zanga-zangar EndSARS a Najeriya.

A karar da Jigon APC din ya shigar ya nemi kotun ta tilastawa Dorsey da Kamfanin Twitter biyan sa kudi Dala Biliyan 1.

A cikin karar wacce lauyan sa, Abbas Ajiya ya gabatar, Adamu Garba ya nemi kotun ta tilastawa shugaban kasa Buhari ya dauki matakan dakatar da Dorsey da kuma shafin Twitter daga daukar nauyin masu zanga-zangar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here