Mutane Huɗu Sun Rasa Rayukan Su Yayin Zanga-Zangar EndSARS a Kano

0
211

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, anyi zargin mutane hudu sun rasa rayukan su a hannun ɓata gari a Kano yayin zanga-zangar EndSARS a yankin Sabon Gari da ke Kano.

Zanga-Zangar ENDSARS wacce aka yi mako na biyu ana yin ta don kawo karshen cin zarafin da ake zargin yan sanda da yi.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa masu zanga-zangar sun taru da misalin karfe 9 na safe a yau Talata sai dai yan daba sun far wa masu zanga-zanga.

Rahotannin sun bayyana cewa an kone shaguna da ababan hawa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here