Majalisar Dattijai Ta Buƙaci Buhari Ya yiwa Ƴan Najeriya Jawabi Kan Zanga-Zangar EndSARS

0
169

Majalisar dattijai a yau Talata ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yiwa yan Najeriya jawabi kan batun zanga-zangar EndSARS a kasarnan.

Ta kuma bukaci matasan dake zanga-zangar da su dakata da yin zanga-zangar don bawa gwamnatin tarayya dama ta saurari bukatun su.

Majalisar ta yi kiran ne bayan kudurin da Sanata Biodun Olujumi na PDP ya gabatar gaban ta.

An shiga Mako na biyu kenan ana gudanar da zanga-zangar ta EndSARS in da ta rikiɗe ta koma rikici a wasu jihohin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here