Kwankwaso Ya Ƙaddamar Da Makarantar Firamare Yayin da Yake Bikin Murnar Zagayowar Ranar Haihuwar Sa

0
218

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ƙaddamar da makarantar Firamare ta ƴaƴan Fulani, wacce ya gina a garin Gangaren Gayya, dake Karamar hukumar Rano a jihar

Yayin da yake jawabi lokacin bikin ƙaddamar da makarantar wanda ya gudana a Gangaren Gayya yau Talata, Kwankwaso ya ce kimanin ɗalibai 300 ne aka sanya a makarantar.

Ya ce ya yanke shawarar gyara makarantar ne, wacce tsohuwar makarantar Islamiyya ce, don bunkasa ilimin yaran dake rayuwa a yankin.

Kwankwaso, wanda ya kasance Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya a Majalisa ta Takwas ya ce yana da kudurin tallafawa ilimin al’ummar yankin har zuwa matakin jami’a.

Ya ce kaddamar da makarantar ya na daga cikin shagulgulan bikin murnar zagayowar ranar haihuwar sa karo na 64.

Makarantar, wacce gidauniyar Kwankwasiyya ta gina, ta na da wuta mai amfani da hasken rana kuma ta na da gine-gine da suke da ajujuwa 6.

“Babbar manufa ta ce samar da ilimi ga al’umma, musamman ya’yan talakawa.

” Wannan makarantar ta jima anan, amma ta kasance ta Islamiyya. Sai naga akwai bukatar gyara ta ta zama babbar makarantar wacce za’a dinga koyar da ilimin Boko da na Addinin Musulunci”, inji shi.

Tsohon gwamnan ya bukaci al’ummar yankin da su amfani da makarantar yadda yakamata, sannan ya yi kira da su kula da makarantar don amfanar kan su.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here