SICPARDN: Aikin mu hada kai da jami’an tsaro dan magance ayyukan ta’addanci a Najeriya

0
188

 

Daga Rabilu Abubakar, Gombe

Mataimakin babban Daraktan kungiyar nan ta sa kai dan samar da tsaro na farin kaya ta SICPARDN Searchlight initiatives for community peace advocacy & rural development bangaren tsaro da bada horo, Bashir Sale, yace aikin Kungiyar su shi ne hada kai da jami’an tsaro dan rage miyagun ayyuka a tsakanin al’umma.

Bashir Sale, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da wakilin mu a Gombe kan aikace-aikacen su a madadin babban Daraktan kungiyar kuma wanda shi ne ya kafa ta Prince Okinlloye Ogunmudede,

Yace a jihar Gombe cikin wannan shekarar ta 2020 kawai sun samu rahotannin fyade da aka yi wa kananan Yara sama da guda 20 da suka turawa helkwatar Yan sanda dan daukar matakin da ya dace.

Bashir Sale, yace a kowacce rana suna rubuta rahoton sirri kan abubuwan dake gudana suna turawa jami’an tsaron farin kaya na DSS, sannan rahoton da ya shafi na harkar kwaya kuma suna turawa hukumar NDLEA dan bin sawu da daukar matakin da ya dace akai.

Ya kara da cewa a cikin shekarar 2019 da ta gabata sun shiga harkar babban zaben da ya gabata sun taka rawa sosai wajen hana sayen kuri’u inda a jihohi kamar Kano da Jigawa da Katsina da Enugu da Benin sun kama mutane da yawa masu sayen kuri’u kuma jihohin sun yaba da aikin da suka yi.

Sale, yace ko a ranar Lahadin da ta gabata, sun samu rahotanni guda uku daga jihar Kano da suka shafi fyade da kuma harkar buga jabun kudi kuma yanzu haka suna ci gaba da bibiyar lamarin dan gano masu laifin.

Har ila yau ya kara da cewa a cikin wannan shekara ta 2019 sun samu rahoton wasu mutane masu buga jabun dalar Amurka da suka gudanar da bincike suka kama su suka turawa hukumar tsaron farin kaya ta civil defence inda su kuma suka fadada binciken suka gano asalin mai laifin a jihar Adamawa, da wani mutum guda a babban birnin tarayya Abuja.

Bashir Sale, ya ci gaba da cewa manufofin wannan kungiya ta sa kai shi ne tana karfafa yunkurin kore laifuffuka a cikin al’umma ta hanyar tattaunawa dan wanzar da zaman lafiya.

Tana kuma inganta kishin kasa a zukatan mutanen kasar dan cusa musu kaunar ta da zai hana su aikata miyagun laifufuffuka.

Daga nan sai Bashir Sale, ya kuma yi amfani da wannan damar ya yi kira ga al’ummar kasa baki daya wajen basu rahotannin sirri da zai kai su ga cin nasara a aikin su wajen shawo kan batagari masu aniyar banza a ransu, sannan kuma ya hori masu son aikata laifuffuka da cewa su sani duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here