Salihu Tanko Yakasai Ya Nemi Afuwar Ganduje

0
343

Mai bada shawara na musamman kan kafafen yada labarai ga gwamna Ganduje, Salihu Tanko Yakasai ya nemi afuwar Gwamnan bayan ya dakatar da shi bisa sukar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A Makalar da ya rubutu tare da aikata zuwa kafafen yada labarai ranar Lahadi, Salihu Tanko Yakasai ya nemi afuwar gwamnan bisa sanya a yanayin rashin jin dadi sakamakon ra’ayib kashin kansa.

Ya ce “Ga Mai gidana, Mai girma Gwamna, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, OFR, Ina son yin amfani da wannan damar wajen neman afuwa bisa sanya mai girma gwamna cikin yanayin rashin jin dadi sakamakon ra’ayin kashin kai na.

” Hakika abu ne da ban taba tunanin faruwar sa, kuma bana farin cikin faruwar sa. Ba wai alaqar mai gida da hadimin sa ce kadai ke tsakanin mu da mai girma gwamna ba; ina da alakar da da uba tsakanin mu da kai mai girma gwamna.

“Hakika, Na yaba da goyan bayan ka gare ni a shekaru biyar da suka wuce, zan kuma ci gaba da zama mai biyayayya gare ka da kuma hidimtawa jihata da kasata ta hanyar gwamnatin ka a kowanne irin mataki”, inji shi.

Salihu Tanko Yakasai ya kuma yi bayanin cewa, yan Najeriya su ci gaba da addu’a ga Najeriya don ta zama kasaitacciya.

Idan za’a iya tunawa dai, a ranar 11 ga watan Oktoba ne, Ganduje ya bada umarnin dakatar da Salihu Tanko Yakasai bayan sukar shugaban kasa Buhari a shafin sa na Twitter.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here