Mazauna Unguwar Kofar Mata Dake Kano Na Zanga-Zanga Bisa Zargin Ƴan Sanda Da Kashe Wani Matashi

0
201

Matasan Unguwar Kofar Mata, Karamar hukumar Birnin Jihar Kano na gudanar da zanga-zanga yanzu haka bisa zargin jami’an ƴan sandan Constabulary da kashe wani matashi dan unguwar.

Wakilin jaridar PRIME TIME NEWS da ya isa wajen zanga-zangar da misalin karfe 10:30 na safe ya tarar da matasa dauke da kwalaye sun datse hanyar zuwa kasuwar kantin kwari a jihar.

Yayin da ya zanta da wasu daga cikin masu zanga-zangar wanda ya nemi a boye sunan sa ya shaidawa cewa, jiya da daddare jami’an yan sandan Constabulary na Area Command, Shahuchi Division ” Suka zo unguwar tare da kama wani matashi wanda yake kwance yana kallo, kana suka yi masa duka da ya yi sanadiyyar mutuwar sa”.

Jaridar Prime Time News ta yi kokarin jin ta bakin Kakakin Rundunar ƴan sanda reshen jihar Kano amma haƙan ta bai cimma ruwa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here