Kwankwaso Ya Buɗe Sabon Gidan Rediyo a Kano

0
242

 

Sashin Hausa na BBC ya wallafa labarin cewa, tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya buɗe sabon gidan rediyo a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.

Gidan rediyon mai suna Nasara FM zai fara watsa shirye-shiryensa na gwaji a kan mita 98.5 a zangon FM daga ranar Alhamis, ta hanyar sanya karatun alkur’ani mai girma.

Shugaban gidan rediyon Maude Rabiu Gwadabe wanda tsohon ma’aikacin BBC ne, ya ce suna fatan samun karɓuwa a wajen al’ummar jihar.

Gidan rediyon ya samu amincewar hukumar kula da kafafen watsa labarai ta Najeriya wato NBC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here