Jami’ar Yusif Maitama Sule Kano Za ta Samar Da Ƙarin Ɓangarorin Karatu – Kurawa

0
221

Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa, sabon shugaban jami’ar Yusif Maitama Sule Kano, ya ce makarantar za ta samar da karin Fannonin karatu don cimma bukatar jihar a fannin ilimi.

Kurawa, wanda ya yi magana yayin tattaunawa da kafafen yada labarai ranar Litinin a Kano, ya ce jami’ar za ta bada muhimmanci ga jin dadin dalibai da ma’aikatan ta don bunkasa bangaren ilimi.

Ya ce walwalar dalibai da ma’aikata zai kasance abin da zai fi mai da hankali yayin zaman sa a jami’ar.

Shugaban jami’ar ya yi alkawarin samar da ƙudurori da shirye-shirye don tabbatar da kwasa-kwasan da jami’ar ta ke yi sun samu tantancewa.

Yayin da yake yabawa gwamna Abdullahi Umar Ganduje bisa samar da ayyukan bunkasa ilimi a jihar, Kurawa ya bukaci masu ruwa da tsaki da su tallafawa jami’ar don ganin ta cimma ƙudurorin ta.

Sannan ya nemi hadin kan ma’aikata, da malamai wajen ganin ya ciyar da jami’ar gaba.

An nada Farfesa Kurawa a matsayin shugaban jami’ar a ranar 17 ga watan Oktoba.

Kafin nadin nasa shi ne shugaban kwalejin fasaha ta jihar Kano.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here