An Naɗa Shahararren Ɗan Jarida A Matsayin Janar Manaja Na Sabuwar Rediyon Nasara a Kano

0
188

An naɗa shahararren dan jarida kuma tsohon ma’aikacin gidan Rediyon BBC, Maude Gwadabe a matsayin janar manaja na sabon gidan Rediyo a Kano.

Rediyon mai suna Nasara ta samu sahalewar kama aiki daga hukumar kula da kafafen yada labarai ta NBC a wannan makon kan mita 98.5 a zangon FM.

Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da Ko’odinetan kafa tashar, Alhaji Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar.

Ya ce Rediyon Nasara an kafa ta ne don don bunkasawa tare da kare al’amuran al’umma ta hanyar nagartattun shirye-shirye da labarai ingantattu.

Ana saran dai tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso ne zai kaddamar da sabuwar tashar Rediyon a dai-dai lokacin da yake bikin murnar zagayowar ranar haihuwar sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here