Zanga-Zangar EndSARS ta Raba Kan Najeriya – Gwamnan Bauchi

0
150

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya ce kasarnan ta rabu sakamkon zanga-zangar #EndSARS a fadin kasarnan.

Bala Mohammed, wanda ya zanta da yan jarida a wata tattaunawa a masaukinsa na Yelwan Duguri, da ke karamar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi, jim kadan bayan ya kada kuri’ar sa a zaben kananan hukumomi a yau Asabar.

Gwamnan ya bukaci kafafen yada labarai da su yi amfani da rahotannin da suke hadawa wajen hada kan yan Najeriya a fannin zanga-zangar adawa da cin zarafin da yan sanda ke yi, inda ya kara da cewa yan sanda suna da iyakar su, kuma kasarnan na bukatar yan sanda su samar da zaman lafiya.

Ya ce, “Najeriya ta rabu yanzu a batun zanga-zangar adawa da rundunar SARS da da ake yi. Ku, a matsayin ku na yan Jarida, kar ku harzuka lamarin, sai dai hada kan yan Najeriya ta hanyar yada labaran da suka dace wadanda baza su ruru wutar rikici ba”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here