
Kungiyar matasan Arewa ta jihar Katsina, ta ce gwammatin shugaba Buhari ta gaza a jihar da ma kasa baki daya bisa gaza kare dukiya da rayukan jama’a.
Kungiyar wacce ta bayyana hakan a wata sanarwa da tafitar bayan taron tattauna matsalolin tsaro da kungiyar ta yi a jiya Asabar a Katsina, sannan kuma sun yi kira ga sauya tasiwirar tsaron kasarnan.
Matsalolin da aka tattauna yayin zaman sun hada da sabbin hare-haren da yan bindia ke kaiwa, kashe-kashe da garkuwa da muatane a jihar.
Sanarwar ta na dauke ne da sa hannun shugaban kungiyar, Jamilu Charanchi da Sakataren ta, Abubakar Kabir.