Rashin Tsaro: ‘A Chechi Jama’a’ – Inji Aisha Buhari

0
124

Matar shugaban Kasa, Aisha Buhari, ta nemi kawo karshen matsalar tsaro a yankin Arewacin Najeriya.

Matar shugaban kasar a wani sako da ta wallafa tare da aika wani gajeran bidiyo a shafin Twitter, tare da rubutun #Achechijamaa.

Bidiyon mai sakanni 22 ya nuna hotunan shugaba Buhari tare da hafsoshin tsaro a zaman tattaunawa da suka yi daban-daban, yayin da waka ke tafiya a ciki wadda mawakin Hausa, Adam A Zango ya yi.

A cikin wakar dai ana fadin “Arewa na Kuka”, in da mawakin ya nemi Buhari ya mayar da hankali kan abinda mutane ke fadi tare da kawo karshen kashe-kashe a Arewa.

“Muna mutuwa, Baba. Suna kashe mu, Baba. Arewa na kuka, jinin mu na kwarara, ana kashe mutanen mu”, Inji mawakin.

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan gamayyar kungiyoyin Arewa sun nemi matasa su tsunduma zanga-zanga a jihohi 19 na Arewa don jawo hankalin gwamnati kan kashe-kashen da ake yi a yankin.

Haka kuma maganar ta matar shugaban kasa na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake gudanar da zanga-zangar kira ga sake yin garambawul ga rundunar yan sanda.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here