NECO Ta Ɗage Ranar Zana Jarrabawar Sakamakon Zanga-Zangar EndSARS

0
260

Hukumar shirya jarrabawar kammala Sakandire ta kasa(NECO) , ta ɗage jarrabawar da za’a fara gobe Litinin 19 ga watan Oktoba, har sai zuwa 16 ga watan Nuwamba.

Hakan na ɗauke ne cikin wata sanarwa da babban jami’in yada labarai da hulda da jama’a na NECO, Azeez Sani ya fitar a yau Lahadi.

Azeez Sani ya ce an dauki matakin ne sakamakon zanga-zangar #ENDSARS da ke gudana wacce ta ke shafar sufurin ababen hawa.

Ya yi bayanin cewa, zanga-zangar ta shafi fitarwa tare da rarraba kayan jarrabawar.

Sanarwar ta ce ” Ana sanarwa da al’umma musamman wadanda za su zana jarrabawar NECO cewa an daga jarrabawar Computer Practical da aka tsara za’a yi ta ranar Litinin 19 ga watan Oktoba, karfe 10 zuwa 1 na rana. Wannan jarrabawa yanzu za ayi ta ne ranar 16 ga watan Nuwamba.”

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here