Ana Zanga-Zangar EndSARS ne Don Rusa Gwamnatin Buhari – Shekh Jingir

0
95

Shugaban majalisar malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’a Wa’ikamatus Sunnah (JIBWIS), Shekh Sani Yahaya Jingir, ya yi zargin cewa zanga-zangar EndSARS da ake yi, shiri ne da aka shirya don tarwatsa gwamnatin shugaba Buhari da yankin Arewacin kasarnan.

“A bayyana yake cewa zanga-zangar EndSARS shiri ne na kawar da gwamnatin Buhari da yankin Arewacin kasarnan. Na fadi hakan ne saboda Lokacin da masu zanga-zangar suka nemi a soke rundunar SARS, gwamnati ta yi hakan, amma masu zanga-zangar su ka ci gaba da yi, har wasu ma suna kiran shugaban kasa ya yi murabus. Hakan na nuna ma cewa akwai makarkashiya a zanga-zangar”, Inji Shekh Jingir.

Malamin ya yi zargin ne a ranar Juma’a yayin gabatar da Sallar Juma’a a masallacin Yantaya dake garin Jos na jihar Plateau.

“Bama goyan bayan zanga-zangar EndSARS saboda babu gaskiya a ciki. Siyasa ce kawai. Muna kira ga mutane su kaucewa shigar ta. Abinda muke bukata yanzu shi ne mu yi addu’ar hadin kan kasar mu da tawo karshen matsalar tsaro a cikin al’umma.”

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here