Mutane Uku Sun Rasa Ransu a Zanga-Zangar #EndSARS a Jihar Osun

0
81

A kalla mutane uku ne suka rasa ransu a garin Osogbo a yau Asabar, yayin zanga-zangar #EndSARS.

Haka kuma, an lalata motoci da dama na tawagar gwamnan Osun, Adegboyega Oyetola bayan harin da ake zargin yan daba sun kai wajen zanga-zangar.

Jaridar THE PUNCH ta rawaito cewa, matum daya ya rasu a asibitin koyarwa na Ladoke Akintola.

Wani likita a Asibitin da ya nemi a boye sunan sa ya shaidawa jaridar cewa, mutumin ya mutu ne sakamakon harbin bindiga.

Haka kuma jami’an tsaro sun tabbar da cewa mutane biyu sun rasu a garin na Osogbo.

“Mutane uku suna Mutuware yanzu haka. An harbe mai kayan kidan mu da wasu mutum biyu”, inji wani mamba a kungiyar #RevolutionNow, Olaoluwa Owoeye.

Jim kadan bayan isar gwamnan wajen zanga-zangar, sai jami’in kula da kungiyar ta #RevolutionNow, Olawale Bakare ya nemi gwamnan da ya nemi afuwar sa bisa kin shiga zanga-zangar wacce aka yi tsawon kwanaki tara ana yi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here