Masu Zanga-Zangar EndSARS Sun Tara Tallafin Kuɗi Sama Da Naira Miliyan 77

0
147

Kungiyar Feminist Coalition daya daga cikin kungiyoyin dake jagorantar zanga-zangar EndSARS, ta ce ta samu tallafin kudi sama da Naira Miliyan 77 don gudanar da zanga-zangar adawa da rundunar SARS.

Kungiyar wacce kudurorin ta suka hada da “yaki da rashin adalci ta hanyar zanga-zangar lumana, hada tallafin kudi, da yada manufa ta kafar sadarwar zamani” ta bayyana hakanne a wata sanarwa da ta fitar yau wacce ta yi mata suna da ‘Rahotan ci gaba – 15 ga watan Oktoba, 2020’.

Kungiyar ta ce an tattara kudin ne ta hanyar yan Najeriya dake bada gudunmawa.

Sanarwar ta ce ” tsawon mako guda matasan Najeriya ke gudanar da zanga-zangar lumana, inda suke neman a rushe rundunar SARS da kuma kawo karshen cin zarafi da yan sanda ke yi.

“Kamar kowa, mun yanke shawarar mu bada gundumawa daga bangaren mu da kuma taimakawa wajen yaki da rashin adalci ta hanyar samar da kudade don ganin an gudanar da zanga-zangar lumana da kuma kare lafiyar Yan Najeriya dake yin abinda hakkin su ne, ta hanyar samar da abinci, ruwa da sauran kayan ciye-ciye, safar rufe baki da hanci, magani ga masu zanga-zanga.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here