Jami’ar Yusuf Maitama Sule Kano Ta Samu Sabon VC

0
156

Majalisar gudanarwar jami’ar Yusuf Maitama Sule Kano, ta amince da nadin Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa a matsayin sabon shugaban Jami’ar.

A wata takarda mai kwanan wata 16 ga watan Oktoba, 2020 mai dauke da sa hannun shugaban majalisar gudanarwar jami’ar, Farfesa Muhammad Yahuza Bello, ta bayyana cewa nadin ya fara aiki ne daga yau.

Wasikar ta kuma bayyana cewa, sabon shugaban jami’ar, zai yi tsawon shekara 5.

Kafin nadin Farfesa Mukhatar Kurawa dai shi ne shugaban kwalejin Fasaha ta jihar Kano wato Kano state Polytechnic.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here