#EndSARS: Anyi Kutse a Shafin Hukumar NBC

0
270

Kungiyar masu kuste(Hacking) mai suna Ananymouse, sun yi kutse a shafun Twitter na hukumar dake kula da kafafen yaɗa labarai ta NBC.

Kungiyar masu kutsen sun yi amfani da shafin hukumar wajen goyan bayan zanga-zangar #EndSARS.

“Mu #Anonymous mu karbe ragamar shafin twitter na hukumomin Najeriya don nuna goyan baya ga zanga-zangar ENDPOLICEBRUTALITY”, inji kungiyar a wani bayani da ta wallafa a shafin hukumar NBC.

Haka kuma sun yi kira ga Yan Najeriya da su fadi sauran hukumomin Najeriya da suke so ayiwa kutse.

Sannan masu kutsen sun yi ikirarin tona asirin gwamnatin Najeriya.

Hukumar ta NBC ta tabbatar da yin kutsen inda ta bayyana a shafin ta na Facebook cewa, jama’a su yi watsi da duk abinda suka gani.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here