
Wasu da ba a san ko su waye ba wadanda suke kaddamar da hari kan shafukan sadarwa na gwamnati, sun yi kutse a shafin babban bankin Najeriya, CBN.
Kutsen dai anyi shi ne don nuna goyan baya ga masu zanga-zangar EndSARS.
Shafin na babban bankin Najeriya a yau juma’a ya nuna rubutun cewa “500 – Internal server erro. There is a Problem with resource you are looking for, and it cannot be displayed”.
Ma’ana shafin na nuna cewa akwai matsala babu damar shigar sa a yanzu.
Ba’a samu Mai magana da yawun babban bankin na CBN, Isac Okoroafor, a waya domin yin bayani kan lamarin.
Tun da farko dai masu kutsen sun yi kutse a shafukan gwamnati da suka hada da na hukumar kula da kafafen yada labarai, NBC.