Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Tarayya Ta Bada Umarnin Buɗe Sansanin Masu Yiwa Ƙasa Hidima

0
151

Gwammatin tarayya ta amince da buɗe sansanin masu yiwa ƙasa hidima(NYSC) a faɗin ƙasarnan daga ranar 10 ga watan Nuwamba.

Ministan Ci gaban matasa da harkokin wasanni, Mista Sunday Dare ne ya bayyana hakan a shafin sa na Twitter yau Alhamis.

“An amince da buɗe sansanin horar da masu yiwa kasa hidima daga ranar 10 ga watan Nuwamba. Za’a sanya cikakkun matakan kariya daga cutar COVID-19.”

A ranar 18 ga watan Maris ne dai gwamnatin tarayya ta bada umarnin rufe sansanin horar da masu yiwa kasa hidima a fadin kasarnan bayan ɓullar cutar Korona.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here