Yajin Aikin Kungiyar Malamai Ta ASUU ne Ke Bunkasa Zanga-Zangar EndSARS – Gwamnatin Tarayya

0
167

Gwamnatin tarayya ta ce,  ci gaba da rufe jami’i’o wanda yajin aikin kungiyar malaman makarantu ta ASUU ya haifar ya taimaka wajen bunkasa zanga-zangar EndSARS.

Sannan ta yi bayanin cewa ba ta duba yuwuwar sauya tsarin biyan albashi na IPPIS da tsarin UTAS kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka rawaito.

Ministan kwadago, Dr. Chris Ngige wanda ya bayyana hakan yau a Abuja a taron sulhu da yake gudana yanzu haka tsakanin kungiyar malamai ta ASUU da gwamnati, ya yi kukan cewa, yajin aikin ya kawo nakasu ga harkoki karatu manyan makarantun kasarnan.

Rahotannin na nuni da cewa har zuwa yanzu da ake wallafa wannan labarin, kungiyar ta ASUU da gwamnatin tarayya suna tattaunawa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here