Yajin Aiki: Matsayar Da Aka Cimma Tsakanin ASUU Da Gwamnatin Tarayya

0
185

An daga Zaman tattaunawar da aka yi tsakanin kungiyar ASUU da Gwamnatin tarayya kan batun janye yajin aiki zuwa 21 ga watan Oktoba.

Yajin aikin da kungiyar ta fara tsawon watanni 6 da su ka wuce, shi ne babban dalilin da ya sa jami’o’i ba su dawo karatu ba bayan janye dokar kulle ta Korona.

Zaman tattaunawar na yau yazo ne bayan zaman tattaunawa na baya da kungiyar ta yi da shugaban majalisar dattijai.

A zaman tattaunawar, Mista Ngige ne ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya, yayin da shugaban kungiyar ASUU, Biodun Ogunyemi ya wakilci kungiyar.

Haka kuma, tattaunawar ta jiya Alhamis ba ta kai ga cimma matsayar janye yajin aikin ba, ta kare ne kan samar da kudade ga jami’o’i don inganta su kamar yadda wata sanarwa daga ma’aikatar kwadago ta bayyana.

“Gwamnati, duk da faduwar tattalin arziki sakamakon annobar Korona, ta bada damar biyan kudi Naira Biliyan 20 ga makarantu zuwa karahen shekarar 2021, kuma kungiyar ASUU ta amince da damar yayin da za ta gabatar da ita ga mambobin ta don dubawa tare da dawowa ranar Laraba 21 ga watan Oktoba.”

Sanarwa da ma’aikatar ta fitar ta kara da cewa, ministan ilimi, Malam Adamu Adamu, zai ci gaba da tattaunawa da ministar Kudi da tsare-tsare kan takardar da ta aikawa shugaba Buhari na samar da wasu hanyoyin samarwa da jami’o’i kudade.

Haka kuma, a batun bukatar kungiyar ASUU na biyan Alawus din malaman jami’ar daga shekarar 2019 wanda ya kai Naira Biliyan 40, babban Akanta janar na kasa zai fitar da Naira Biliyan 30 ranar 6 ga watan Nuwamba ko kafin ranar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here