A Yau Ministan Ƙwadago Zai Tattauna da ASUU Don Kawo Ƙarshen Yajin Aikin Da Ƙungiyar Ke Yi

0
161

A yau Alhamis, Ministan Kwadago, Dr. Chris Ngige, zai tattauna da shugabannin kungiyar Malaman jami’i’o ta kasa ASUU a kokarin kawo karshen yajin aikin da kungiyar ta shafe watanni shida ta na yi.

Wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar, Mista Charles Akpan ya fitar ta ce Ngige zai yi tattaunawar da ASUU a Abuja.

Kungiyar ASUU dai ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani biyo bayan adawa da tsarin gwamnati na biyan albashi ta cikin tsarin IPPIS.

Kungiyar ta jaddda cewa sai dai ayi amfani da tsarin UTAS.

Amma bayanai na nuni da cewa da yuwuwar yajin aikin ya zo karshe bayan kungiyar ASUU ta tattauna da shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Ahamd Lawan.

Tattaunawar ta hada da ministan ilimi Malam Adamu Adamu, Babban Akanta janar na kasa, Ahmed Idris da shugabancin kungiyar ASUU bisa jagorancin Farfesa Biodun Ogunyemi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here