Rahoto na Musamman: Mazauna Garin Saye Dake Kano Sun Rungumi Magungunan Gargajiya Sakamakon Taɓarɓarewar Fannin Lafiya a Garin

0
239

… Suna Fama da Lalacewar Makarantu da Hanyoyi.

… Akwai Makarantar da Malamai Biyu ne Kaɗai suke koyar da Ɗalibai

 

 

Safiyar ranar Litinin ce a cibiyar lafiya matakin farko dake garin Saye, wani kauye da ake cin kasuwa a karamar hukumar Bichi, sama da Kilo Mita 30 daga Birnin Kano.

Da misalin karfe 7 na safiyar ranar Litinin din, marasa lafiya sun cika a cibiyar lafiyar don duba lafiyar su, sai dai su yi jira na tsawon awanni uku ba tare da ganin ma’aikacin lafiya daya ba a cibiyar. hatta kofar shiga cibiyar a rufe take ba tare da masu gadi ba.

Yayin da wakilin Jaridar PRIME TIME NEWS ya isa garin Saye, kauyen da yake da adadin mutane 1, 000 ya ga marasa lafiya, wadanda yawancin su suna cikin mawuyacin hali sai dai babu wani ma’aikacin lafiya da zai duba su.

Wata mata mai ciki mai suna Amina, ta na cikin mawuyacin hali amma an bar ta a kwance kan dandamalin kasa ba tare da Likita ya duba ta ba.

Amina, wacce da kyar ta ke magana ta ce ta shafe tsawon kwanaki 2 ba tare da ta yi fitsari ba.

“Na zo nan tun karfe 7 na safe, tun lokacin ina jiran ma’aikatan lafiya. Eh ba daya daga cikin su da yazo. Ina cikin wannan hali tsawon kwanaki amma ba tare da samun kulawar likitoci ba” Inji Amina.

Wata mara lafiyar mai suna Maimuna, wacce tayi jiran ganin likita yayin da take fama da ciwo mai tsanani, ta ce ta shafe tsawon awanni uku amma ba ta ga koda mutum daya daga cikin ma’aikatan cibiyar lafiyar ba.

Maimuna, wacce ta ke fama da cutar zuciya, ta ce likitoci sun fada ma ra cewa yawan shan maganin gargajiya ne ya haifar mata da ciwon.

Ta yi bayanin cewa ta zabi yin amfani da maganin gargajiya sakamakon gazawar cibiyar kula da lafiya a garin, inda ta kara da cewa yawancin mazauna garin an tilasta musu amfani da maganin gargajiya a garin.

“Suna na Hussain daga Tanga-Iyaw. Na kawo dan’uwana wannan cibiya don duba lafiyar sa sai dai kamar kullum ba su zo a kan lokaci ba kuma wasu lokutan suna fada mana cewa babu magani”, inji wani mazaunin garin.

” Yawancin Kauyuka anan suna amfani da itatuwan gargajiya da sauran hanyoyin maganin gargajiya don taimakar kan mu. Ba wanda ke taimakar mu, ina tunanin gwamnati ta manta da mu.

“Dayawan mata masu dauke da juna biyu daga kauyuka takwas suna zuwa nan don haihuwa. Bamu da zabi saboda nan ne kadai muke da shi, duk da yawan mu, cibiyar bata aiki”, Inji Hussain.

“Kamar yadda zaka iya gani, duk wani waje a cibiyar lafiyar a rufe yake sai wajen da marasa lafiya ke tsayuwa tare da cikowar mutane kan tabarma, da yan kalilan din gadon kwanciya, babu matashin kwanciya ga marasa lafiya”, inji shi.

Wakilin mu ya kuma lura da cewa cibiyar lafiyar na cikin halin ko in kula wacce hatta bandakin da jama’a ke shiga na cikin kazanta.

Haka kuma, Jaridar PRIME TIME NEWS ta samun bayanin cewa cibiyar lafiyar ba ta da isassun ma’aikara kuma likita daya ne yake duba marasa lafiya sau daya duk mako.

“Likitoci anan basa aiki tsawon awannin 24, suna budewa ne yayin da suke jin dadi sannan su tashi 12 na rana wani lokacin karfe 2 na rana”, inji mazauna garin.

Wakilin mu ya kuma wuce zuwa garin Badume, inda ya zanta da wani mai sana’ar Achaba, Malam Iliyasu wanda ya dauke shi zuwa kauyen Tukuibi, wani gari dake da yawan mutane dubu 1, sai dai babu hanya kuma babu rufaffun ajujuwan daukar karatu.

Iliyasu ya shaidawa Jaridar PRIME TIME NEWS cewa duk da akwai hanya daga babbar hanyar Badume, sai dai ba ta kai ga garin Saye ba, ” Babu hanyoyi a dukkan kauyukan dake nan yankin, babu wacce ma zata kai ka Saye, sakamakon hakan ana yawan samun hatsari a hanyoyin”.

Wani garin bayan kauyen Tukuibi shi ne Bankaura, wannan kauyen yana da tarin jama’a sai sai Jaridar PRIME TIME NEWS lura cewa makarantar garin tana da gini biyu ne kacal tare da malamai guda biyu dake koyar da daruruwan dalibai.

“Yawancin mutanen yankin nan manoma ne, muna samar da Tumatir da sauran kayan amfanin gona da ake amfani da su yau da kullum, kusan manyan motoci 200 suna zuwa nan wajen fitar da kayayyakin noma zuwa birni da makotan jihohi”.

“Ina rayuwa anan yankin tsawon shekaru 30 amma hanya, makarantu, cibiyar kula da lafiya sun lalace in takaice ma zance, komai na tabarbarewa anan kuma cewa muna jin muna jihar Kano. Yakamata gwamnati ta saurari kukan mu ta kuma zo ta taimake mu don inganta yankin mu”, inji Malam Iliyasu.

Wakilin jaridar PRIME TIME NEWS ya zanta da wani malamin makaranta wanda ya nemi a boye sunan sa inda ya ce suna da dalibai sama da 2000 amma babu abun zama ko daya da gwamnatin Kano ta kawo musu, hatta daliban ajin karshe na Firamare suna zaune ne a kasa ko kan tabarmi suma malamai suna jinge a haka.

Ya bayyana cewa yayin da gwamnatin jihar Kano ta bude makarantu tare da umartar hukumomi da su bi ka’idojin kariya daga cutar Korona, Firamaren Saye an bata abun wanke hannu guda uku kacal, da bokitin ruwa, kuma ba’a bamu safar rufe hanci da baki ko guda daya ba”.

“Ban sani ba, Amma gwamnatin jihar Kano ta sanya mu yarda cewa babu cutar COVID-19 kawai karya ce”, inji malamin.

Yayin da wakilin mu ya nemi malaman makarantar su nuna masa bandakin dalibai, sun ki amincewa amma alamu sun nuna cewa ginin bandakin yana fama da matsala kuma ciyayi sun rufe shi.

Zailani da Yahaya Mugaji mazauna garin Saye, sun bayyana cewa duk wani abu na saukin rayuwa baza ka ganshi a garin ba, inda suka ce suna rayuwa cikin wahala.

” An sha fada mana alkawarin kanzon kurege tun muna yara cewa gwamnati za ta dube mu. Tsawon shekaru da dama al’umma suna cikin duhu, mun shafe tsawon watanni 8 ba wutar lantarki a Saye.

Yayin zantawa da wani dattijo a garin, ya fadawa jaridar PRIME TIME NEWA cewa halin matsi da al’ummar garin ke fuskanta abun damuwa ne kuma babu wani abu ci gaba na ku zo ku gani a yankin.

“Firamaren Saye ta shafe tsawon shekaru, ajujuwa da dama basu da kofofi, tagogi da kujera. rufi ya fada. Gyran da kuka ga anyi a makarantar ‘yan mata al’ummar garin ne suka yi”.

“Anan muna hada tallafin kudi saboda akwai bukatar ya yan mu su je makaranta. Mun kai ziyara da dama ga hukumomi a jihar Kano, mun mika takardu ga gwamnatin Kano kan bukatun mu amma bama ganin su sai lokacin zabe. Wasu lokutan, muna mamakin cewa bama daga cikin yankin Kano..wani lokacin ma muna tunanin bama daga cikin yan Najeriya”.

“Komai anan ya zama abin takaici…”

Yayin da aka tuntubi babban Sakataren hukumar kula da lafiya matakin farko, Dr. Tijjani Hussain ya shaidawa jaridar PRIME TIME NEWS cewa yana sane da halin da cibiyoyin lafiya suke ciki a yankin kauyukan kuma akwai sauye-sauye da za ayi kwannan.

Dr. Tijjani wanda ya yi magana ta bakin jami’in hulda da jama’a na hukumar, Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa a daren ranar Talata, ya ce sabon babban sakataren hukumar ya yi alkawarin duba yanayin da cibiyoyin lafiya matakin farko a yankin karkara da kin halartar ma’aikatan lafiya da sauran matsaloli.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano za ta ci gaba da bunkasa kiwon lafiya a jihar.

Kashi na biyu na wannan labarin na nan tafe…..

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here