Najeriya ce Tafi Kowacce Ƙasa Samar da Shinkafa da Rogo a Faɗin Duniya – Nanono

0
291

Sabo Nanono, Ministan noma da raya karkara, ya ce daga shekarar 2022 gwamnatin tarayya za ta hana shigo da Madara cikin kasarnan.

Nanono ya bayyana hakanne yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja. a taron ranar Abinci ta duniya na shekarar 2020.

Ya yi bayanin cewa ma’aikatar ta na shirya tsare-tsare don tabbatar da samar da abubuwan da ake bukata na fitar da Madara.

“Muna shiri a wannan ma’aikata, nan da shekara biyu masu zuwa zamu hana shigo da madara cikin kasarnan. Ku tambaye ni saboda me: muna da shanu miliyan 25 a wannan kasar da za su iya samar da lita miliyan 5 a kullum”, inji shi.

Nanono ya kuma ce Najeriya ce kasar da tafi samar da shinkafa da Rogo a duniya.

Ya ce ” Najeriya ta hana shigo da ita inda ta kafa shirin samar da shinkafa don karfafa gwiwar samar da shinkafa a cikin gida”.

Ministan ya kuma yi bayanin cewa, farashin kayayyakin abinci da ya yi tashin gwauran zabi saboda annobar COVID-19 zai sakko nan da yan watanni.

Nanono ya kara da cewagwamnatin tarayya ta hanyar shirin ta na (APPEALS) ta ware Naira Biliyan 600 a matsayin bashi ga manoma don tallafa musu a fadin kasarnan.

Ya ce ana saran manoma miliyan 2 da dubu dari 4 ne za su amfana da tallafin don bunkasa noman su.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here