Majalisar Ɗinkin Duniya Ta yi Magana Kan Zanga-Zangar EndSARS

0
188

Majalisar Dinkin Duniya a jiya Talata ta yi kira da masu zanga-zangar End SARS su kasance suna yin ta cikin zaman lafiya.

Edward Kallon, babban wakilin majalisar dinkin duniya a Najeriya, ne ya yi kiran a shafin sa na Twitter.

Majalisar dinkin duniyar ta kara nuna goyan bayan ta ga hadin kan Najeriya.

Haka kuma ta yabawa yunkurin gwamnatin tarayya na yin garambawul ga rundunar yan sanda.

Majalisar ta ce aikin garambawul din zai dau lokaci.

“Na bibiyi ci gaban da ake samu dangane da zanga-zangar EndSARS. Kokarin gwamnati na soke rundunar da yin garambawul ga rundunar yan sanda a bun yabbawa ne.

” Lamarin zai dau lokaci. Ina kira ga matasa da su kasance masu son zaman lafiya. Majalisar dinkin duniya ta shirya wajen tallafawa don ganin Najeriya ta kasance mai zaman lafiya da kwanciyar hankali”, inji shi.

Tunda farko dai an soki hukumomin kasarnan kan hana kawo tsaiko ga zanga-zangar ta EndSARS sai dai daga baya gwamnatin ta amince da bukatun masu zanga-zangar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here