Gwamnan Jihar Legas Ya Gabatarwa da Buhari Bukatun Masu Zanga-Zangar EndSARS

0
147

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara jaddada kokarin sa na yiwa rundunar yan sanda garan bawul.

Sanwo-Olu ya tattauna da shugaban kasar a Abuja Awanni kadan bayan ya shiga zanga-zangar EndSARS da aka yi yau a Legas.

Gwamnan ya gabatar da bukatun masu zanga-zangar ga shugaban kasa wadanda a ciki har da kawo karshen cin zarafin da yan sanda ke yi.

Ya ce:

“Yau na gana da Shugaban Kasa Buhari don gabatar ma sa da bukatun masu zanga-zangar #EndSARS. Shugaban kasa ya kara bayyana aniyar sa na yiwa rundunar yan sanda garanbawul gabadaya.

“A yau, shugaban kasar ya amince da kafa kwamitin bincike da ya hada da shugabannin kungiyoyin ci gaban al’umma wanda zai yi duba kan zarge-zargen cin zarafi da yan sanda suka yi. Za’a gane amfanin wannan zanga-zanga zan kuma ci gaba da aiki wajen kare hakkin duk wani dan jihar Legas”, Inji Gwamnan.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here