Buhari Ya Naɗa Mataimakiyar sa A Matsayin Kwamishiniya A Hukumar Zaɓe ta INEC

0
174

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dattijai ta tabbatar da mataimakiyar sa ta musamman kan sha’anin kafafen yada labarai na zamani, Lauretta Onochie , a matsayin kwamishiniya a hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC.

Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, ne ya karanta wasikar shugaban kasar yau Alhamis a zauren majalisar.

Sauran wadanda Buhari ya nema su zama Kwamishinonin sun hada da Farfesa Mohammed Sani daga Katsina, Farfesa Kunle Ajayi daga Ekiti da Seidu Ahmed daga Jigawa.

Onochie dai ta shara wajen wallafa bayanan dake jawo cece-kuce a kafar sadarwa ta zamani.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here