Za’ayi Zaɓen Ƙananan Hukumomi a Jihar Kano

0
220

Shugaban hukumar zabe ta jihar Kano, Farfesa Garba Ibrahim Sheka ya shaidawa manema labarai cewa, hukumar KANSIEC ta sanya ranar 16 ga watan Janairun shekarar 2021 a matsayin ranar da za’a gudanar zaben ƙananan hukumomin jihar.

Farfesa Garba Ibrahim Sheka shi ne ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudana a shalkwatar hukumar dake Kano.

Jihar Kano na da kananan hukumomi 44, fiye da kowacce jiha a kasar nan, haka kuma harkar siyasa da zabe a jihar ya kan fi Ko wace jiha jan hankali idan za a gudanar da shi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here