Gwamnonin APC Huɗu Sun Bada Tallafin Naira Miliyan 152 Ga Jami’ar Musulunci a Jigawa

0
212

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na jihar Jigawa, Abubakar Bagudu na jihar Kebbi, Aminu Masari na Katsina da Simon Bako Lalong sun bada gudunmawar Naira Miliyan 152 ga jami’ar Assalam dake Hadejia a jihar Jigawa.

Gwamnonin Jigawa, Katsina da Kebbi sun bayar da Naira 50 kowannen su yayin da gwamnan jihar Plateau ya bayar da Naira Miliyan 2, Gwamna Badaru ne ya sanar da hakan a madadin gwamnonin yayin bikin kaddamar da ginin jami’ar a karamar hukumar Hadejia dake jihar Jigawa.

Alhaji Muhammad Badari Abubakar ya jinjinawa kungiyar Jama’atul Izalatul Bida’a Wa’ikamatus sunna (JIBWIS) bisa zabar jihar Jigawa wajen samar da jami’ar. “Dabarar abar ci gaba ce kuma zamu taimaka wajen ganin kammaluwar aikin nan”. Inji shi.

Ya ce, ” Ilimi mabudin ci gaba ne a kowacce al’umma a wannan duniyar sannan wannan aikin zai taimaka wajen samar da ci gaba a wannan karamar hukuma da jiha baki daya, shi yasa dole na yabawa kungiyar Izala bisa yin wannan aikin a Jigawa”.

Gwamnan ya ce idan aka kammala jami’ar musuluncin za ta dinga bada gurbin karatu ba ga yan jihar Jigawa kadai ba har da makota sannan kuma za ta zama jami’a ta biyu ta musulunci bayan jami’ar Al-Qalam dake jihar Katsina.

Shi ma ana sa jawabin, Ministan Sadarwa Dr. Ali Isah Pantami, wanda ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari a taron ya ce shugaban kasar ya yi alkawarin tallafawa wajen kafa jami’ar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here