Ganduje Ya Bada Umarnin Komawa Manyan Makarantu a Kano

0
101

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya amince da sake bude manyan makarantun jihar daga ranar 26 ga watan Okutoba.

Kwamishiniyar ilimi mai zurfi ta jihar Kano, Mariya Mahmoud Bunkure ce ta sanar da hakan a yau Litinin.

Sanarwar ta biyo bayan komawa makarantun Sakandire da Firamare a safiyar yau Litinin.

Kwamishiniyar ta kuma umarci ma’aikata da daliban makarantun su tabbata sun bi matakan kariya daga cutar COVID-19.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here