Ayyukan Mazaɓu: Ba na daga cikin Ƴan Majalisar Dake Ɗumama Kujera -Joɓe

0
233

Shugaban kwamitin majalisar wakilai kan raya karkara kuma mai wakiltar kananan hukumomin Dawakin -Tofa, Tofa da Rimin Gado, Injini Tijjani Abdulqadir Jobe ya ce zai kare hakkin yan mazabar sa.

Jobe ya ce “Bazan so na zama irin dan majalisar da sunan sa yake na kasa ba”.

Yayin da yake jawabi jim kadan bayan kammala kaddamar da bude hanyar Rimin Gado zuwa Gulu wanda aka yi a karamar hukumar Rimin Gado jiya Lahadi, Jobe ya bayyana cewa tsarin wakilcin sa ba irin nayin surutun da bashi da amfani bane, sai dai wanda zai kawo aikin ci gaba.

Dan majalisar ya yi bayanin cewa hakkin da al’umma su ka dora masa na wakiltar su tsawon shekara hudu a majalisar wakilai hakan yana nuna tasirin wakilcin sa.

Ya ce, yin alkawarin da babu shi ko yin alkawari da shifcin gizo ba ya haifar da da mai ido ga wanda aka zaba bisa gaskiya da kwarin gwiwar zai wakilci al’ummar sa a lokacin da suke bukatar ayyukan raya kasa don daddana roman dimukuradiya.

Dan majalisar ya yi nuni da cewa ba wani dan siyasa na gari da zai so ya kasance cikin masu gazawa.

Ya kuma yi bayanin cewa gabatar da ayyukan raya mazabu don gamsar da al’ummar sa ya zama kashin baya na yarda da shi da al’umma suka yi tun zaman sa dan majalisa.

Jobre ya kara da cewa, a shekara daya da ta gabata ya gabatar da ayyuka 48 daban-daban da suka hada da haka rijiyar burtsatsai, wutar Sola da ajujuwan kararu kari kan hanyoyi da ya gina.

Ya kuma bayyana cewa an bayar da kwangilar gina hanyar Rimin Gado zuwa Gulu don taimakawa manonaman dake yankin wajen fito da amfanin gonar su zuwa kasuwannin.

Ya ce za’a sanya ido kan aikin don tabbatar anyi shi da inganci.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here