Akwai yuwuwar Cutar Korona Ta Ƙara Ɓulla Karo Na Biyu – Gwamnatin Tarayya

0
132

Kwamitin fadar shugaban kasa kan yaki da annobar Korona ya gargadi yan Najeriya kan yuwuwar sake bullar cutar Korona karo na biyu.

Shugaban kwamitin kar ta kwana kan yaki da cutar COVID-19 na fadar shugaban kasa, Boss Mustaphata ne ya bayyana hakan a yau Litinin yayin jawabin kullum-kullum da kwamitin ke yi a Abuja.

Ya ce ba wata kasa da ta samu rigafin da zai sa cutar baza ta sake bulla ba.

Ya shawarci yan Najeriya da su sanya a ran su cewa cutar na iya dawowa, inda ya yi bayanin cewa hanyar kaucewa dawowar ta kadai shi ne bin matakan kariya da aka sanya.

“Kwamitin yaki da Korona yana farin ciki kasancewar ana ci gaba da bude harkokin kasuwanci, amma ya na gargadin cewa a ci gaba da karantar irin ci gaban da aka samu a kasashen turai da sauran sassan duniya, ba wata kasa da za ta ce tana da rigakafin sake bullar cutar karo na biyu matukar aka gaza bin ka’idojin da aka shimfida, akwai bukatar yan Najeriya su gane hakan kuma su shirya. Fatan mu da addu’ar shi ne kar hakan ya kasance.”

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here