Yanzu-Yanzu: An Soke Rundunar SARS

0
152

 

Babban sifeton ‘yan sandan na kasa Mohammed Adamu, ya soke rundunar da ke yaƙi da fashi da makami  wato SARS.

Ya bayyana hakan ne a wani jawabin kai tsaye ga manema labarai a ranar Lahadi.

Soke rundunar ya biyo bayan jerin zanga-zangar da aka ɗauki kwanaki ana yi a wasu jihohin ƙasarnan, inda ko a yau ma sai da aka yi irin wannan zanga-zangar a Ingila kamar yadda Sashin Hausa na BBC ya rawaito.

‘Yan ƙasarnan dai suna zargin rundunar ta SARS da azabtarwa da kisa ba bisa ƙa’ida ba da saɓa dokokin aiki.

A baya dai gwamnatin ƙasarnan ta ce ba za ta soke rundunar ba, sai dai ta yi mata sauyi ko kuma kwaskwarima kan yadda rundunar ta ke gudanar da ayyukanta, inda ko a kwanakin baya sai da Shugaban Majalisar Dattawa,  Ahmed Lawan ya ce ba zai yiwu a soke rundunar ba sai dai a sauya tsarinta.

Hakazalika wasu daga cikin ƙusoshin gwamnatin ƙasarnan da wasu gwamnoni da muƙarraban shugaban ƙasar na da irin wannan ra’ayi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here