Ozil Ya Goyi Bayan Zanga-Zangar #EndSARS a Najeriya

0
105

Dan wasa Mesut Ozil, a yau Lahadi ya bayyana goyan bayan sa ga masu yin zanga-Zangar #EndSARS a Najeriya.

Dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ya bayyana hakan ne a shafin sa na twitter.

“Na damu da jin abin da ke faru a Najeriya. Mu mayar da hakan abin tattaunawa da zai dau hankali a ko ina #EndSARS – ina nuna damuwa ta ga duk wanda abun ya shafa”, ini shi.

Dan wasa Ozil ba ya jin kunyar bayyana ra’ayin sa kan manyan batutuwan dake faruwa a duniya kuma yana daga cikin yan wasam da suka yi Allah wadai da kasar China kana yadda ta ke cin zarafin Musulmai.

Su ma yan wasan Najeriya da suka hada da Ahmed Musa da Alex Iwobo sun goyi bayan zang-zangar ta #EndSARS.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here