Ganduje Ya Dakatar Da Salihu Tanko Yakasai Bisa Sukar Shugaban Kasa Buhari

0
206

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje a yau Lahadi ya dakatar da mataimakin sa na musamman kan kafafen yada labarai, Salihu Tanko Yakasai bisa caccakar shugaban kasa Muhammadu Buhari a shafukan sadarwa na zamani.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, wanda ya bayyana umarnin gwamnan a wata sanarwa da aka aikowa jaridar PRIME TIME NEWS yau a Kano, ya ce dakatarwar ta fara aiko nan take.

Ya ce duk da cewa hadimin gwamnan ya na da damar bayyana ra’ayin sa shafun sa na kafar sadarwa ta zamani, amma kasancewar sa na matsayin wanda al’umma ke kallo zai zama mai wahala a iya ban-bance ra’ayin kashin kan sa ko kuma ra’ayin gwamnati kan abinda ya shafi al’umma.

Haka kuma gwamnan ya gargadi masu rike da mukaman siyasa da su kaucewa yin bayanan da za su kawo rudanin da bai da alfanu wanda kuma zai haifar da rashin zama lafiya.

Sanarwar ta bayyana irin kokarin gwamna Ganduje na goyan bayan manufofi da tsare-tsaren shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Idan za’a iya tunawa dai, a jiya ne Mataimaki ga Ganduje kan kafafen yada labarai, Salihu Tanko Yakasai ya ce Shugaba Buhari ba ya tausayawa al’ummar Najeriya.

Salihu Yakasai, wanda ya wallafa a shafin sa na twitter, @dawisu, yana bayyana ra’ayin sa ne kan gazawar shugaba Buhari na yin jawabi kan korafe-korafe da ake yi da kuma zanga-zangar adawa da rundunar SARS.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here